Likitan da ya kwashe shekaru 7 a hannun 'yan ta'adda ya kubuta
Hukumomin Australia sun tabbatar da kubutar likitan kasar mai shekaru 88 da aka yi garkuwa da shi a yammacin Afrika, kuma tuni aka hada shi da iyalan sa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A sanarwar da ministar harkokin wajen Australia Penny Wong ya fitar a jiya Juma’a, ta ce Kenneth Elliott, na cikin koshin lafiya kuma tuni an hada shi da mai dakin sa Jocelyn da ‘ya’yan sa.
A watan Janairun shekarar 2016 ce aka yi garkuwa da shi da mai dakin sa a Arewacin Burkina Faso iyaka da kasashen Mali da Nijar, inda suke da asibitin da suke kula da shi sama da shekara 40.
Sai dai bayan makonni 3 da garkuwa da su, an saki mai dakin ta sa, yayin da shi kuma ya kwashe tsawon shekaru 7 a hannun masu garkuwa da shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu