Isa ga babban shafi

An kashe kauyawa 12 a yammacin Burkina Faso

Fararen hula akalla goma sha biyu ne aka kashe a wani sabon hari da wasu da ake zargin mayakan jihadi ne suka kai a wani kauye da ke yammacin Burkina Faso da ke kan iyaka da kasar Mali, kamar yadda wani jami’i da mazauna yankin suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa a yau Asabar.

'Yan ta'addan MUJWA a Burkina Faso masu alaka da Al Qaida.
'Yan ta'addan MUJWA a Burkina Faso masu alaka da Al Qaida. Reuters
Talla

Mazauna yankin sun bayyana cewa, maharan sun farwa kauyen ne da yammacin jiya Juma, inda suka kashe na kashe tare da kona gidaje.

Wannan harin na zuwa ne kwanaki bayan wani kazami da aka kai a arewacin kasar mai fama da hare-haren ‘yan ta’addan da suka tsallaka kasar daga Mali, inda aka kashe kimanin mutane 20.

Majiyoyi sun ce ko a jiya Juma’a ma an kai wasu hare-hare a gabashin Burkin Fason, an kashe mutane 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.