Isa ga babban shafi

An sake kashe mutane 20 a wasu sabbin hare-hare a Burkina Faso

Akalla mutane 20 ne suka mutu a wasu jerin hare-haren da aka kai wasu kauyuka da ke fama da rikici a Burkina Faso, kamar yadda majiyar tsaro da kuma wasu mazauna yankunan suka tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP.

Shugaban mulkin sojin Burkina Faso Ibrahim Traoré.
Shugaban mulkin sojin Burkina Faso Ibrahim Traoré. REUTERS - VINCENT BADO
Talla

Wani mazaunin yankin ya ce maharan da ke kan babura sun kai harin ne a kauyukan Pelle da Zanna da kuma Nongfraire, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 25. 

Majiyar tsaro ta tabbatar da hakan, sai dai ta ce adadin wadanda suka mutu bai wuce 20 ba.

Burkina Faso, wacce ta yi fama da matsalar juyin mulki karo biyu a shekarar bara, na fama da matsalar tsaro daga masu tsa-tsauran ra’ayin addini bayan da suka ketara kasar da Mali a shekarar 2015. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.