Wakilan sojin Sudan sun isa Saudiyya don tattaunawar tsagaita wuta
Rundunar sojin Sudan ta aike da tawagar da za ta wakilce ta a birnin Jeddah na Saudiyya don tattaunawar tsagaita wuta, wanda Amurka da Saudiyya suka shirya.
Wallafawa ranar:
Bayanin haka ya fito ne a wata sanarwar da sojin Sudan din ta fitar a daren Juma’a.
A yammacin Juma’a ne tawagar ta baro Sudan Zuwa birnin Jeddah, a yayin da sojin da ma abokan hammayarsu na RSF suka ce za su tattauna tsagaita wuta ce kawai bisa dalilai na jinkai amma ba don kawo karshen rikicin kacokan ba.
Gwamnatocin Amurka da Saudiyya sun tabbatar da cewa za a fara tattaunawa kai tsaye a tsakanin sojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na musamman a ranar Asabar din nan.
A wata sanarwa, Amurka da Saudiyya sun bukaci dukkan bangarorin da ke rikici da juna su yi la’akari da kasarsu da jama’arsu a yayin tattaunawar tsagaita wutar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu