Isa ga babban shafi

Rikicin Sudan ya jefa sha'anin kiwon lafiya cikin bala'i

Rikicn da ake gwabzawa a Sudan na ci gaba da jefa bangaren kiwon lafiya yanayi na tabarbarewa, inda kawo yanzu asibitoci ke ci gaba da rufewa saboda rashin kayan aiki. 

Wakilan MDD kenan da ke ganawa kan makomar Sudan
Wakilan MDD kenan da ke ganawa kan makomar Sudan © Ibrahim Mohammed Ishak / Reuters
Talla

Wata jami’ar kiwon lafiya a babban asibitin lardin Bahri Dakta Safaa Aboush, ta ce sakamakon matsaloli, tuni wasu asibitoci suka daina aiki baki. 

"Saboda wannan fada da ake yi, yanzu haka ina makale ne a cikin wani asibiti yau kusan kwanaki 10. Wani lokaci na kan share tsawon kwanaki uku ba tare da na samun ruwan da zan yi wanka ba, ba abinci, ba ruwa balantana wutar lantarki," in ji Dakta Safaa. 

"Muna son taimaka wa marasa lafiya amma ba za mu iya ba saboda rashin kayan aiki. Akwai mutane da dama da ke fama da cututuka kansa da cutar kodar amma ba za su iya samun kulawa ba a asibiti." 

Ta ce, akwai mutanen da ake kawo wa da raunuka ciki har da karaya amma ba su da kayan aikin da za su iya taimaka musu. 

A cewar Dakta Safaa, asibitoci na cikin wani yanayi, saboda ba za a iya kula da hatta wadanda ke fama da cututuka kamar tarin asma ko hawan jini ba, duk wadannan na rayuwa ne a cikin hadarin, wadanda ake fargabar za su iya rasa rayukan su saboda bala'in da rikicin ya haifar a kasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.