Isa ga babban shafi

Biden ya yi barazanar kakaba takunkumi kan rikicin Sudan

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi barazanar kakaba sabbin takunkumai kan masu ruwa da tsaki a rikicin Sudan, muddun bangarori biyu dake rikici da juna basu kawo karshen yakin da ake gwabzawa a kasar ba, yayin fadan da ake gwabzawa musamman a Khartoum ya shiga kwana ta 20.

Shugaban Amurka Joe Biden.19/04/23
Shugaban Amurka Joe Biden.19/04/23 © AP / Patrick Semansky
Talla

Shugaban na Amurka Joe Biden ya rattaba hannu kan wata dokar zartaswa ranar alhamis, wacce ke kara fadada damarsa ta sanya takunkumi kan wadanda ke barazana ga zaman lafiya da tsaron Sudan.

Biden wanda bai bayyana sunayen wadanda ya yi baranzar kakabawa takunkumin ba, yace dole ne akawo karshen rikicin da ya lakume rayukan al’umma da basu ji ba basu gani ba, tare da shirya mika mulki ga farar hula.

An kashe mutane da dama

Daruruwan mutane ne aka kashe a Sudan tun bayan da aka fara gwabza fada a ranar 15 ga watan Afrilu tsakanin dakarun Hafsan Sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan da tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo dake jagorantar rundunar Rapid Support Forces (RSF).

Kuma yayin da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta ke kawo karshe cikin dare, rundunar sojin kasar ta ce a shirye ta ke ta mutunta sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki bakwai da aka cimma, sai dai babu wata sanarwa daga bangaren RSF.

Sa’o’i kafin kafin sabuwar yarjejeniyar tsagaita wutar ta soma aiki, shaidun a birnin Khartoum sun bayyana cewa ana ci gaba da musayar wuta da cin karar abubuwa masu fashewa a birnin mai mutane miliyan biyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.