Isa ga babban shafi

Amurka ta bukaci a dakatar da sabon rikicin da ya kunno kai a Sudan

Kasashen duniya sun bukaci a yi gaggawar dakatar da sabon tashin hankalin da ya kunno kai a tsakanin sojoji dadakaru na musamman a Sudan.  

Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken. REUTERS - ELIZABETH FRANTZ
Talla

 

Sakataren harkokin wajen Amurkan Antony Blinken ya ce kasar sa ta damu matuka da rahotannin rikicin da take samu daga Sudan.  

A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter daga taron ministocin kula da harkokin ketare na kungiyar kasashe G7 da ke gudana a kasar Vietnam, Blinken ya ce wajibi ne sojojin Sudan da hukumomin tsaron suka dakatar da tahomugar da suka fara, inda ya bukace su da su hau teburin sulhu domin magance sabanin da ke a tsakaninsu. 

Jami’an kiwon lafiya a Sudan din sun ce a halin da ake ciki tuni rikicin ya yi ajalin mutane uku a babban birnin kasar Khartoum da kuma wasu biranen da sabon rikicin ya barke, yayin da mutane tara suka jikkata. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.