Isa ga babban shafi

Kazamin fada ya barke a birnin Khartoum duk da batun tsagaita bude wuta

A yau lahadi kazamin fada ya barke tsakanin sojojin Sudan da dakarun sa-kai a birnin Khartoum, a daidai lokacin da batun tsagaita bude wuta na kwanaki uku da ba a taba mutuntawa a kasa ba, ke shirin kawo karshe.

Janar al-Burhan da Janar  Hemedti, masu fada da juna a Sudan
Janar al-Burhan da Janar Hemedti, masu fada da juna a Sudan AFP - ASHRAF SHAZLY
Talla

Miliyoyin 'yan kasar Sudan ne suka makale a cikin gidajen su a wani lokaci da ake fuskantar ruwan bama-bamai daga jiragen sama tun bayan barkewar rikicin kasar a ranar 15 ga watan Afrilu tsakanin sojojin Janar Abdel Fattah al-Burhane da na biyu, Janar Mohamed Hamdane Daglo, wanda ke ba da umarni ga dakarun Rapid Support Forces (FSR).

Rikicin kasar Sudan
Rikicin kasar Sudan AP - Marwan Ali

A alkawarin bangarorin biyu tsagaita bude wuta  a wannan wa’adi na biyu bai hana a ji karar harbi a birnin Khartoum da sauran yankuna ba, musamman yankin Darfur. Wannan tsagaita wutar za takawo karshe a yau lahadi  tsakar dare da misalin karfe 10 na dare.

Jama’a sun bayyana farin cikin su da samun labarin jirgin farko dauke da "ton takwas" na agaji da suka hada da "kayan aikin tiyata" wanda ya sauka a kasar Sudan inda ake da marasa lafiya kusan 1,500" a kasar da akasarin asibitoci ba sa aiki saboda yaki.

Wani ginin babbar kasuwar Khartoum a Sudan
Wani ginin babbar kasuwar Khartoum a Sudan REUTERS - MOHAMED NURELDIN ABDALLAH

Jirgin wanda kuma ke dauke da ma'aikatan jin kai, ya taso ne daga Amman ya sauka a tashar jiragen ruwa na Sudan, wani gari da ke gabar teku mai tazarar kilomita 850 daga gabashin Khartoum, a cewar hukumar agaji ta ICRC. An rufe sararin samaniyar Sudan tun ranar 15 ga watan Afrilu yayin da aka fara gwabza fada a filin tashi da saukar jiragen sama na Khartoum.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.