An kai wa jirgin Turkiyya hari a Sudan
Ma'aikatar tsaron Turkiyya ta bayyana cewa an harbi wani jirgin sojinta da ke aikin kwashe 'yan kasar daga Sudan.
Wallafawa ranar:
An harbi jirgin mai lamba C-130 ne yayin da ya nufi sansanin sojin saman kasar da ke Wadi Seidna domin kwashe 'yan kasar da ke birnin Khartoum, a cewar ma’aikatar.
Sai dai ta ce jirgin ya sauka lafiya, kuma ba bu wanda ya samu rauni a sanadin harbin, kamar yadda kafar yada labaran kasar TRTWorld ta ruwaito.
A yayin da take mayar da martani kan wannan lamari, rundinar sojin Sudan ta zargi dakarun sa-kai na RSF da aikata wannan aika-aika, sai dai RSF din ta musanta hakan.
A wata sanarwa da rundinar ta RSF ta fitar, ta ce “ba gaskiya bane cewa da ake yi mu muka kai wa jigin Turkiyya hari. Tun a daren jiya muka fara mutanta yarjejeniyar da aka yi da mu".
"Ta yaya ma za a ce dakarunmu ne suka kai hari kan jirgin kwashe ‘yan Turkiyya bayan mu ne muka taimaka wurin kare ‘yan kasar a kwanan nan, da ma kwashe sauran ‘yan kasashe a dukkan yankunann babban birnin Sudan".
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu