Isa ga babban shafi

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gudanar da zaben Libya a watan Yuni

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci bangarorin da ke rikici da juna a Libya su amince da ganin an gudanar da zabe a sassan kasar kafin nan da tsakiyar watan Yunin shekarar nan.

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Libya Abdoulaye Bathily.
Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Libya Abdoulaye Bathily. AP - Yousef Murad
Talla

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman da ke shiga tsakani a Libya Abdoulaye Bathily yayin wani jawabinsa a karshen mako ya yi kira da bangarorin biyu da su amince da gudanar da zaben kasar wanda aka gaza aiwatarwa a watan Disamban 2021.

Bathily dan Senegal wanda tun cikin watan Oktoban bara ke fuskantar suka daga bangarorin biyu na Libya sakamakon matsin lambarshi na ganin sun cimma daidaito wajen kulla yarjejeniya a tsakaninsu.

Yayin wani jawabin kai tsaye ta gidan talabijin Abdoulaye Bathily ya kare tayin da ya gabatarwa bangarorin biyu da cewa idan har suka aminta da cimma yarjejeniya ko shakka babu nan da tsakiyar watan Yuni za a iya gudanar da zaben shugaban kasa a Libya tare da kawo karshen rarrabuwar kan da ake fuskanta.

Tun bayan hambarar da gwamnatin Moamer Khadhafi a shekarar 2011 Libya ke fuskantar rikici bayan da kowanne bangare ya samu jagora wanda ya kunshi gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya da kuma tsagin babban kwamandan Sojojin kasar Khalifa Haftar.

Tuni dai Firaminista Abdelmajid Dbeiba ya amince da tayin na Bathily don ganin an gudanar da zabe a Libyan yayinda ya jaddada bukatar ganin an hana duk wani da ke da takardun zama dan kasa a kasashe 2 iya tsayawa takara, bukatar da kai tsaye ke kalubalantar takarar Haftar a zaben, wanda ke da takardar zama a Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.