Isa ga babban shafi

An ceto bakin-haure sama da 200 a gabar tekun Libya

Kungiya likitocin kasa da kasa ta Faransa ta yi ikirarin ceto mutane 237 a gabar tekun Libya da ke yunkurin tsallakawa zuwa turai.

Bakin -haure da dama ne ke tsallakawa zuwa Turai daga gabar tekun Libya.
Bakin -haure da dama ne ke tsallakawa zuwa Turai daga gabar tekun Libya. REUTERS/Stringer TPX IMAGES OF THE DAY
Talla

Kungiyar ta ce mambobin ta ne suka hango jirgin da bakin hauren ke ciki yana tangal-tangal a ruwa tare da Shirin nutsewa, nan take kuma suka yi kokarin ceto su.

Ceto wadannan  mutane ke da wuya kuma jim kadan aka sake hango wani jirgin roba, makare da mutane shima da ke Shirin tsallakawa turai cikin hadari, ba kuma tare da bata lokaci ba shima aka ceto mutanen, abinda ya bada adadin jimillar mutanen zuwa 237.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.