Isa ga babban shafi

EU da Morocco za su karfafa huldar dakile kwararar bakin-haure zuwa Turai

Kungiyar Tarayyar Turai EU da Morocco sun ce za su kara hada gwiwa don yaki da safarar mutane, bayan da akalla bakin-haure 23 suka mutu a kokarin shiga yankin Melilla na kasar Spain.

'Yan sandan Morocco yayin kokarin hana daruruwan bakin-haure kwarara cikin yankin Melilla na kasar Spain.
'Yan sandan Morocco yayin kokarin hana daruruwan bakin-haure kwarara cikin yankin Melilla na kasar Spain. AP - Javier Bernardo
Talla

Wadanda suka rasa rayukan nasu dai na cikin bakin-haure kusan 2,000, akasarinsu daga Sudan, wadanda suka yi kokarin tsallakawa cikin Spain da karfin tsiya daga kasar Morocco.

A waccan lokacin dai, Fira Ministan Spain Pedro Sanchez ya zargi ‘masu fataucin bil'adama' haddasa tashin hankalin.

Ya zuwa yanzu yunkurin bakin-hauren na shiga Turai a baya bayan nan, shi ne mafi muni da aka samu a cikin shekaru da dama a yankunan Ceuta da Melilla na Spain, wadanda ke da iyaka da nahiyar Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.