Isa ga babban shafi

Ana neman daruruwan mutane bayan harin da ya kashe mutane 60 a Burkina Faso

Wata kungiya da ke rajin kare hakkin dan adam a Burkina Faso ta yi ikirarin cewa harin ranar 26 ga watan Fabarairun da ya gabata a yankin Partiaga na gabashin kasar ya kashe mutane akalla 60 amma ba tare da gwamnatin ta bayar da alkaluma ba, yayinda ake ci gaba da laluben wasu daruruwa da suka bace sakamakon firgita daga harin.

Sojojin Burkina Faso  a arewacin kasar.
Sojojin Burkina Faso a arewacin kasar. © ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Babu dai wasu bayanai daga hukumomin Burkina Faso, walau na yankin ko kuma na kasa baki daya da ya tabbatar da harin na watan jiya, wanda kungiyar ta MBDHP ke cewa ya yi matukar muni ga al’ummar yankin na Partiaga.

A cewar kungiyar yayin harin na ranar 26 ga wata, ‘yan ta’addan baya ga kashe fararen hular fiye da 60 sun kuma kone tarin gidaje tare da yin awon gaba da daruruwan dabbobi.

Kungiyar ta bayyana cewa duk da yadda dakarun Soji suka yi gaggawar kai dauki garin amma har yanzu a hukumance Burkina Faso bata fitar da alkaluman mutanen da harin ya shafa ba.

Gwamnan yankin na Partiaga da ke gabashin Burkina Faso Hubert Yameogo ya ce har yanzu ana laluben tarin mutanen da suka bace bayan harin na makwanni 2 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.