An sanya dokar takaita zirga zirga a Burkina Faso don yaki da ta'addanci
Mahukuntan Burkina Faso sun kakaba dokar takaita zirga zirga a tsakiyar yankin gabashin kasar da zummar taimakawa wajen yaki da ta’addanci, kamar yadda wani kundi da kamfanin dillancin labaran Faransa ya gani a wannan Lahadin ya nuna.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Matsalar ta’addanci da aka shafe shekaru da dama ana kokarin dakilewa ta yi sanadin mutuwar dubban fararen hula, ‘yan sanda da sojoji, kana ta tilasta wa sama da mutaane miliyan 2 rabuwa da muhallansu.
Umurnin da ya fito daga ofishin gwamnan yankin gabashin kasar, Kouilga Abert Zongo ya nuna cewa za a takaita zirga zirgar mutane da ababen hawa daga daga karfe 10 na dare zuwa karfe 5 na asuba.
Zongo ya ce wannan dokar takaita zirga zirga za ta taimaka wa dakarun da ke yaki da ta’addancin a kan iyakar kasar da Mali, inda matsalar ta kunno kai tun a shekarar 2015.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu