Isa ga babban shafi

Ana fargabar mutuwar 'yan cirani 73 bayan nutsewar jirginsu a teku

Ana fargabar mutuwar gomman ‘yan cirani sakamakon nutsewar jirgin da ke dauke da mutane fiye da 80 a gabar tekun Libya wadanda ke kan yarsu ta zuwa Turai da nufin samun rayuwa mai inganci.

Wasu 'yan cirani a tsakar teku.
Wasu 'yan cirani a tsakar teku. AFP - SAMEER AL-DOUMY
Talla

Hukumar kula da kaurar baki ta Majalisar Dinkin Duniya IOM ta ce zuwa yanzu mutane 7 kadai aka iya cetowa da ransu, yayinda da dama suka bace a cikin teku bayan nutsewar jirgin na su a jiya talata.

A cewar IOM yanzu haka jami’an agaji na Red Cresent sun iya tsamo gawar mutane 11 daga cikin tekun yayinda ake ci gaba da laluben sauran 73 da suka nutse.

Wata majiyar jami’an tsaron gabar teku a Libya, ta ce jirgin dauke da mutane 80 ya bar tashar jiragen ruwan Qasr Al-Akhyar mai tazarar kilomita 75 daga gabashin birnin Tripoli a yammacin jiya talata yayinda jirgin ya kife tun gabanin kaiwa tsakiyar tekun na Mediterranean.

Hukumar IOM ta ce mutane 7 da aka iya tsamowa da ransu na cikin mawuyacin hali kuma yanzu haka suna karbar kulawar gaggawa a asibiti.

Tsakar tekun Mediterranean na ci gaba da kasancewa mahalaka ga ‘yan ciranin da ke ratsawa zuwa Turai inda ga farkon shekarar nan zuwa yanzu ‘yancirani 130 suka mutu kari kan wasu dubu 1 da 450 da suka mutu a shekarar da ta gabata.

Alkaluma sun nuna cewa daga shekarar 2014 zuwa yanzu fiye da ‘yancirani dubu 17 suka mutu a tekun na Mediterraanean.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.