Isa ga babban shafi

Fafaroma Francis zai gana da yan gudun hijira a Sudan ta Kudu

Fafaroma Francis zai gana da ‘yan gudun hijira a Sudan ta Kudu a yau asabar, bayan da ya bukaci shugabanninsu da su rugumi sabon yunkurin na samar da zaman lafiya a kasar da ke fama da yaki da matsanancin talauci.

Fafaroma Francis a lokacin da yake yiwa wata mata addu'a
Fafaroma Francis a lokacin da yake yiwa wata mata addu'a AP - Gregorio Borgia
Talla

Fafaroma na tare da rakiyar shuwagabannin Cocin Ingila da Scotland, da wakilan sauran mabiya darikar kiristoci biyu na Sudan,kasa mafi karancin shekaru a duniya, Fafaroma Francis ya yi kiyasin a ranar Juma'a cewa "ba za a sake jingine hanyar zaman lafiya ba" ,ya na mai wannan jawabin a gaban mahukunta a Juba babban birnin kasar ta Sudan ta kudu.

Daga shekarar 2013 zuwa 2018, wannan kasa mai mutane miliyan 12 ta yi fama da kazamin yakin basasa tsakanin magoya bayan shugabannin biyu Salva Kiir da Riek Machar, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 380,000.

Duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a shekarar 2018, ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula kuma kasar na da mutane miliyan 2.2 da suka rasa matsugunansu a cikin watan Disamba, sakamakon tashe-tashen hankula da ambaliyar ruwa, a cewar sabon alkalumman da OCHA ta wallafa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.