Isa ga babban shafi

Afirka ta Kudu za ta fara amfani da na'urar tona asirin makaryata

Afirka ta Kudu na shirin fara amfani da na’urar fallasa masu karya kan ma'aikatan da ke aiki a wuraren ajiyar namun daji a wani yunkuri na yaki da matsalar farautar namun daji.

Dabbar karkanda kenan
Dabbar karkanda kenan REUTERS/Thomas Mukoya/File Photo
Talla

Mafarauta, a wasu lokutan suna sa-in-sa da ma’aikatan gandun daji, yayin da suka shiga farauta, abin da a yanzu hukumomi suka ce aika-aikarsu ta rage yawan dabbar karkanda a cikin kasar a shekarun baya-bayan nan.

Domin magance matsalar, hukumar kula da gandun daji ta Afirka ta Kudu, SANParks, ta amince da sabuwar manufar gwajin polygraph ga ma'aikatanta.

Manufar da aka amince da ita a watan Nuwamba ana sa ran za ta fara aiki a farkon shekara mai zuwa, in ji ministar muhalli Barbara Creecy a cikin wata rubutacciyar amsa ga jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance (DA), wacce ta nuna adawa kan mataki.

Afirka ta Kudu tana da kusan kashi 80 na dabbar karkanda da ake da su a fadin duniya.

Sai dai kuma wuri ne da ake fama da farautar karkanda, sakamakon bukatar da ake samu daga Asiya, inda ake amfani da kahon dabbar a matsayin maganin gargajiya.

Kusan karkanda 470 ne aka yi farautar su a fadin kasar tsakanin watan Afrilun 2021 zuwa Maris 2022, a cewar alkaluman gwamnati, abin da ake ganin ya karu da kashi 16 cikin dari a watanni goma sha biyu da suka gabata.

Gandun dajin Kruger na kasar, wani wurin yawon bude ido da ke kan iyaka da Mozambique, ya fuskanci raguwar dabbar karkandan matuka cikin shekaru goma da suka gabata sakamakon farauta.

Adadin dabbar karkanda da ake da su a shekarar 2021 ya kai 2,800, sai dai kusan kashi 70 ne ya ragu idan aka kwatanta da 10,000 a shekarar 2008, a cewar kididdigar SANParks ta kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.