Isa ga babban shafi

Jagororin Afrika ta Yamma sun amince su kafa rundunar soji ta musamman

Shugabannin Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma sun amince su kafa rundunar soji ta musamman a tsakaninsu wadda zata dinga yaki da ‘Yan ta’adda da kuma shawo kan juyin mulkin sojin da ake samu a yankin. 

shugabann Guinée-Bissau, kuma shugaban kungiyar ECOWAS ko  CEDEAO, Umaro Sissoco Embalo.
shugabann Guinée-Bissau, kuma shugaban kungiyar ECOWAS ko CEDEAO, Umaro Sissoco Embalo. © Nipah Dennis / AFP
Talla

Shugaban Majalisar gudanarwar kungiyar ECOWAS Omar Alieu Touray ya sanar da daukar wannan matakin da shugabannin suka yi lokacin taron da suka gudanar karo na 62 a birnin Abuja. 

Touray ya ce shugabannin sun yanke hukuncin kafa wannan runduna ta hadin kai a tsakaninsu domin kai daukin gaggawa duk lokacin da ake bukata, domin tinkarar matsalar tsaro da yaki da ta’addanci da kuma dawo da doka da oda a duk lokacin da aka samu matsala a wata kasa dake yankin. 

Yayin da kasashen Mali da Guinea da kuma Burkina Faso suka fuskanci juyin mulkin soji, kasashe da dama dake yankin da suka hada da Mali da Burkina Faso da Nijar da Najeriya da kuma wadanda ke yankin gabar ruwan Guinea na fama da matsalar fashin teku da kuma barazanar Yan ta’adda. 

Akasari sojojin wadannan kasashe ba sa iya tinkarar ‘yan ta’addan da suka addabi kasashen su, abinda ya sa suka nemi taimakon Majalisar Dinkin Duniya da kasar Faransa da kuma Rasha domin tinkarar matsalar. 

Shugaban gudanarwar ya ce daukar wannan mataki na kafa rundunar ta musamman zai bada damar sake fasalin tsaron yankin baki daya. 

Ana saran shugabannin hukumomin tsaron kasashen ECOWAS su shata yadda rundunar zata kasance a taron da za suyi a watan Janairu mai zuwa, yayin da za’a kuma amince da yadda za’a samar da kudaden tafiyar da ita. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.