Isa ga babban shafi

Kotu a Kenya ta umurci matuka jirgin sama su koma bakin aiki

Kotun masana’antu a Nairobi ta umurci matukan jirgin sama na kaamfanin sufurin jiragen sama na  Kenya  da ke yajin aiki da su koma bakin aiki, bayan sun shafe kwanaki suna yajin aiki wanda ya tilasta soke zirga zirgan jirge da barin dubban fasinjoji a kasa.

Yajin aikin matuka jirgin kamfanin Kenya ya sa fasinja cikin garari.
Yajin aikin matuka jirgin kamfanin Kenya ya sa fasinja cikin garari. © REUTERS/Monicah Mwangi
Talla

Kungiyar matuka jiragen saman Kenya KALPA ta kaddamar da yajin aikin a filin jirgin Jomo Kenyatta na Nairobi a ranar Asabar din da ta gabata, inda ta bijirewa umarnin kotu da ta bayar a makon da ya gabata na nuna adawa da matakin da masana’antu suka dauka a makon jiya.

Mai shari’a Anna Mwaure a ranar Talata ta umurci matukan jirgin Kenya Airways da su koma bakin aikin su,  a safiyar yau, wanda yayi dai dai da 9 ga Nuwamba, 2022 ba tare da wani sharadi ba.

Matakin  ya kara ta’azzara matsalolin da ke addabar sashin , wanda ya kwashe tsahon shekaru yana fuskantar koma baya duk da miliyoyin dalolin da gwamnati ke kashe wa .

Kawo yanzu dai babu wani martani da KALPA ta bayar game da umarnin kotun, wanda mahukuntan kamfanin suka yi na’am da shi, inda suka sha alwashin za su kara zage damtse don  dawo da martaba da mutuncin kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.