Isa ga babban shafi

Liberia: Kunti Kamara ya fara fuskantar tuhumar cin zarafin bil'adama

An fara shari'ar farko kan yakin basasar Laberiya a kasar Faransa, inda tsohon kwamandan 'yan tawaye Kunti Kamara ke fuskantar tuhuma kan laifukan cin zarafin bil'adama da suka hada da azabtarwa.

Kotun daukaka kara da ke birnin Paris a kasar faransa kenan.
Kotun daukaka kara da ke birnin Paris a kasar faransa kenan. AFP PHOTO / JOEL ROBINE
Talla

Zargin da ake yi a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta birnin Paris kan Kamara, mai shekaru 47, ya samo asali ne tun a shekarun 1993 da 1994, a shekarun farko na rikicin baya-bayan nan wanda ya yi sanadin mutuwar 250,000 tsakanin 1989 zuwa 2003.

Rikice-rikicen sun yi sanadin kashe-kashen jama'a, fyade da kuma yayyaka jikin dan adam, a lokuta da dama daga sojoji.

Ana yawan cin zalin jama'a, inda mayaka dauke da muggan makamai cikin maye kuma sare sassan jikin mutane.

A shekara ta 2006 ne aka kafa kwamitin gaskiya da sasantawa don gudanar da bincike kan laifukan da aka aikata a lokacin yakin, amma shawarwarin da aka fitar a shekara ta 2009 sun kasance ba a aiwatar da su ba da sunan wanzar da zaman lafiya.

Kamara, wanda ya bayyana, domin tabbatar da sunansa ga kotun, zai fuskanci hukuncin daurin rai da rai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.