Isa ga babban shafi

An daure wasu sojojin Burkina Faso saboda kisan shugaban dalibai a 1990

Kotu a Burkina Faso ta samu wasu tsaffin jami'an tsaron fadar shugaban kasa uku da hannu a kisan wani shugaban dalibai a shekarar 1990, abinda ya sa ta yanke musu hukuncin daurin shekaru 10 zuwa 30 a gidan yari.

Gilbert Diendéré, jaami'in sojin da yaa jagoranci kama shugabann daaliban.
Gilbert Diendéré, jaami'in sojin da yaa jagoranci kama shugabann daaliban. AFP PHOTO / AHMED OUOBA
Talla

Manyan jami’an tsaron tsohon shugaban kasar Blaise Compaore su uku sun gurfana a gaban kotu ne a ranar Litinin bisa laifin kisan dalibin da ya jagoranci zanga-zangar adawa da shugaban nasu.

A ranar 19 ga watan Mayun shekarar 1990, wasu mutane dauke da makamai suka sace Boukary Dabo, tare da kai shi babban sansanin da ke karkashin  dakarun tsaron fadar shugaban kasa, inda suka azabtar da shi har ya mutu, suka kuma binne  shi a dai sansanin da ke garin Po.

Duk da cewa a shekarar 2000 ne aka fara gudanar da bincike, sai bayan  rikicin da ya haddasa faduwar gwamnatin Blaise Compaore a watan Janairun shekarar 2017 aka gurfanar da su gaban kotu.

Kotu ta sami Janar  Gilbert Diendere da laifin kame ba bisa ka'ida ba, kana ta yi mai daurin shekaru 20 a gidan yari, ta kuma ta ci shi tarar CFA miliyan 1.

Diendere yana zaman daurin rai da rai sakamakon hannun da yake da shi a kisan gilla da aka wa Thomas Sankara a shekarar 1987.

Mamadou Bamba, wanda aka zarga da laifin yanke shawara a kan dalibin da za a kama, an yanke mai hukuncin shekaru 10 a gidan yari da tara CFA dubu 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.