Isa ga babban shafi

Dubban 'yan mata za su cashe a gaban Sabon Sarkin Zulu

Dubban ‘yan mata da yara mata ne ‘yan kabilar Zulu a kasar Afirka ta Kudu ake saran su sheke rawa ranar asabar domin karrama Sabon sarkin su, duk da sukar da ake yi dangane da gudanar da biki na al’adu.

Sarkin Zulu Goodwill Zwelithin (zaune a tsakiyae) tare da shugaban jam'iyyar Inkatha Mangosuthu Buthelezi. 24 ga watan satumba 2019 a birnin Durban.
Sarkin Zulu Goodwill Zwelithin (zaune a tsakiyae) tare da shugaban jam'iyyar Inkatha Mangosuthu Buthelezi. 24 ga watan satumba 2019 a birnin Durban. AFP - RAJESH JANTILAL
Talla

A watan Satumban kowacce sheakara, dubban mata da yan mata daga kabilar Zulu na gangami a tsaunukan garin da ake kira Nongoma, a kudu maso gabashin Yankin KwaZulu-Natal da ke Afirka ta Kudu, domin sheke rawa.

Yayin da ake gudanar da wannan biki, kowace daga cikin matan ko 'yam matan za ta gabatar da kyautar fire ga Sabon Sarkin, yayin da filawar wadanda suka rasa budurcin su ke langwabewa.

Wannan biki dai na daga cikin al’adar Yan kabilar Zulu wanda ya shafi yadda yam mata ke kama hanyar komawa cikakkun mata bisa tarihi da kuma baiwa Sarkin damar zabin sabbin matansa daga cikin mahalarta bikin.

Sabon Sarkin na Zulu, MisuZulu Zulu yana da shekaru 47 a duniya, kuma ana kiran sa da MisuZulu Zulu kaZwelithini.

A watan jiya aka amince shi a matsayin sabon Sarki lokacin gudanar da bikin al’adar Yan kabilarsa, sakamakon rasuwar mahaifinsa Goodwill Zwelithini bayan ya kwashe shekaru 50 a karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.