Al'ummar Zulu na Afirka ta Kudu na murnar nadin sabon sarki
Dubban 'yan kabilar Zulu na Afirka ta Kudu ne suka gudanar da bikin nadin sarautar sabon sarkinsu a wani yanki na lardin KwaZulu-Natal.
Wallafawa ranar:
Misuzulu ka Zwelithini ya sami sarautar ne bayan sama da shekara da rasuwar mahaifinsa Goodwill Zwelithini samakon cutar Covid-19.
Bikin dai na cike da cece-kuce yayin da wasu daga cikin 'yan gidan sarautar suka ki amincewa da nadin nasa inda suka fifitabukaci a zabi guda daga sauran 'yan'uwa a cikin 'ya'yan marigayin sarkin su 28.
Abubuwan al'adun gargajiya da ake gudanarwa kafin nadin sarki, sun hada da wasu lokuta masu tsarki kamar farautar zaki da kuma shiga wata kofar garken dabbobi, shima wuri mai tsarki da ake gabatar da sarki mai jiran gado ga kakannin da suka gabata.
Shugaba Cyril Ramaphosa ya amince da sarkin mai shekaru 47 a matsayin magajin wanda ya mutu, kuma ya kamata kamar yadda da doka tace ya amince da nadin sarautar a hukumance.
Idan sarkin kabilar mafi girma a kasar ba shi da ikon zartaswa, yana da babban ikon akan al'ummarsa fiye da miliyan 11.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu