Isa ga babban shafi

Mayakan Al-Shabab sun kashe fararen hula 19 a kasar Somaliya

Mayakan kungiyar Al-Shabaab sun kashe fararen hula akalla 19 a wani harin da suka kai a tsakiyar kasar Somaliya cikin dare.

Kungiyar ta Al-Shabab ta fitar da sanarwar cewa ta kashe mutanen ne sakamakon zargin su da taimakawa dakarun gwamnati
Kungiyar ta Al-Shabab ta fitar da sanarwar cewa ta kashe mutanen ne sakamakon zargin su da taimakawa dakarun gwamnati (Photo : Mohamed Dahir/AFP)
Talla

Harin dai na zuwa ne makwanni biyu bayan da kungiyar Al-Shabaab da ta dauki tsawon lokaci tana tada kayar baya a kasar Somaliya, ta yiwa wani otel da ke Mogadishu babban birnin kasar kawanya na tsawon sa'o'i 30, inda ta kashe mutane 21 tare da jikkata wasu 117.

Majiyar tsaron kasar ta ce ta ce akalla motoci takwas ne ke tafiya a kan hanyar da ke tsakanin garuruwan Beledweyne da Maxaas a lokacin da maharan suka tare tare da kashe fasinjojin a daren Juma’a zuwa Asabar a kauyen Afar-Irdood.

“Yan ta'adda sun kashe fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba da ke tafiya a cikin daren. Ba mu da cikakken adadin wadanda suka mutu, amma an tattara gawarwaki 19,” kamar yadda wani dan kabilar yankin Abdulahi Hared ya shaida wa AFP.

"Har yanzu ana ci gaba da tattara gawarwakin wadanda suka hada da mata da kananan yara, za su iya wuce 20," in ji Ali Jeyte, gwamnan yankin Hiiraan da harin ya afku.

A wata sanarwa da kungiyar ta Al-Shabaab ta fitar ta ce, ta kai hari kan mayakan wata kabila da ke taimaka wa dakarun gwamnati a baya-bayan nan, inda ta ce ta kashe ‘yan bindiga 20 da kuma wadanda ke yi musu jigilar kayayyaki, tare da lalata motocinsu tara.

Mayakan yankin da jami'an tsaro sun kwato kauyuka da dama daga hannun kungiyar Al-Shabaab a karshen watan Agusta.

Shugaba Hassan Sheikh Mohamud "ya yi kakkausar suka ga munanan ayyukan kisa ga fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba," in ji fadar shugaban kasar ta Somalia a shafin Twitter.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.