Isa ga babban shafi

Gwamnatin Najeriya ta karbe ikon wasu kamfanonin lantarki hudu

Gwamnatin Najeriya ta kwace wasu kamfanonin rarraba wutar lantarki guda hudu, da ke jihohin Kaduna, Kano, Ibadan da kuma Fatakwal.

Turakun wutar lantarki a Najeriya.
Turakun wutar lantarki a Najeriya. © Ventures Africa
Talla

Babban daraktan hukumar kula da kadarorin gwamnatin kasar, Alex Okoh ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya gabatar a taron tattaunawa na hukumar kula da harkokin kasuwanci ta kasar, yana mai cewa an samu nasarar shawo kan matsalar da ta hana karbe kamfanin na Disco da ke Benin.

Taron dai an gudanar da shi ne karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasar wanda ministar kudi, Zainab Shamsuna Ahmed, ta wakilta.

A cikin rahoton da ya gabatarwa taron majalisar, Okoh ya yi bayani kan rangwamen da kamfanin samar da wutar lantarki na Zungeru ya yi, inda ya gayyaci majalisar kula da harkokin kasuwanci da cewa ta lura da matakan da ofishin ya dauka na hanzarta bin diddigin lamarin.

Okoh, ya kuma gabatar da bukatar amincewa da kudirin yin gyara ga dokokin hukumar, musamman a fannin tsarin shari’a, sauye-sauye, da kuma batun cinikayya.

Sauran bangarorin sun hada da karbar dabarun kasuwanci da hada-hadar kudi, hadi da budewa da tantance shawarwarin fasaha, da sauransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.