Isa ga babban shafi

Al-Shabab ta kashe mutane 10 a harin da kai karon farko bayan zaben Somalia

Alkaluman da gwamnatin Somalia ta fitar yau asabar ya tabbatar da mutuwar akalla mutane 10 a farmakin da ‘yan ta’adda suka kai kan wani Otel da ke tsakar birnin Mogadishu a yammacin jiya juma’a.

Otel din da al-Shebab ta kai hari a birnin Mogadishu na Somalia.
Otel din da al-Shebab ta kai hari a birnin Mogadishu na Somalia. REUTERS - STRINGER
Talla

Sanarwar da gwamnatin Somalia ta fitar ta ce ‘yan ta’addan sun bude wuta kan mutanen da ke kokarin tsira da rayukansu bayan tashin bama-bamai har guda biyu da batagarin suka dasa a cikin wasu motoci.

‘Yan ta’addan sun farwa Otal din Hayat ne da ke birnin na Mogadishi wanda ke matsayin matattarar manyan jami’an gwamnatin kasar da ke kokarin samun hutu a karshen mako.

Tuni dai kungiyar al-Shebab ta dauki alhakin harin wanda shi ne irinsa na farko da ta kai tun bayan zaben kasar na watan mayu da ya baiwa shugaba Hassan Sheikh Mohamud nasarar hawa kujerar shugabancin Somalia.

Wani ganau da harin ya faru akan idanunsa, Hussein Mohamed ya ce an dauki tsawon lokaci ana musayar wuta tsakanin tawagar ‘yan ta’addan da jami’an gwamnati a cikin Otel din.

Rahotanni sun ce cikin sanarwar da al-Shabab ta fitar ta yi ikirarin kame wasu jiga-jigan siyasar kasar a farmakin na jiya said ai bata fitar da sunayensu ba.

Farmakin na jiya na zuwa ne a dai dai lokacin da dakarun gwamnati suka karfafa hare-harensu kan ‘yan ta’addan biyo bayan ikirarin shugaba Mohamud na kokarin kawo karshen ayyukan ta’addanci a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.