Isa ga babban shafi

Senegal ta cimma yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan tawaye

Gwamnatin Senegal ta kulla yarjejeniya da ‘yan tawayen Kudancin Kasar da suka lashi takobin ajiye makamansu domin rungumar zaman lafiya na din-din-din.

Yadda aka yi zaman rattaba hannu tsakanin gwamnatin Senegal da 'yn tawayen kudancin kasar a Guinea Bissau kan
Yadda aka yi zaman rattaba hannu tsakanin gwamnatin Senegal da 'yn tawayen kudancin kasar a Guinea Bissau kan © Presidência da República de Guiné-Bissau
Talla

Shugaban ‘yan tawayen na Democratic Forces of Casamance,  Cesar Atoute Badiate ne da wakilin gwamnatin Senegal suka sanya hannun kan yarjeniyar a can kasar Guinea Bissau.

Da ma dai shugaban Senegal Macky Sall ya yi alkawarin bai wa batun  samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin Casamance muhimmanci muddin ya lashe wa’adi na biyu.

A yayin bikin rattaba hannun, shugaban Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embalo ya shaida wa Badiate cewa, za su yi musu rakiyar lalubo zaman lafiya, yayin da ya bayyana damuwa kan adadin mutanen da suka rasa rayukansu da kuma wadanda aka yanke musu gabobin jikinsu ko kuma tilasta musu guje wa kauyensu.

Embalo wanda kuma shi ne shugaban Kungiyar Kasashen Yammacin Afrika ta ECOWAS ya bai wa jagoran ‘yan tawayen tabbbacin cewa, zai yi tsayin-daka wajen ganin an mutunta wannan yarjejeniya ta zaman lafiya.

Kawo yanzu dai, ba a fallasa takardun yarjejeniyar  da bangarorin suka rattaba wa hannu ba.

Tuni shugaba Sall ya yi lale marhabin da yarjejeniyar a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda kuma ya mika godiya ga takwaransa na Guinea Bissau saboda shiga tsakani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.