Barayin shannu sun kashe kauyawa 32 a wani kauyen Madagascar
A Madagascar, akalla kauyawa 32 ne suka kone kurmus inda ake kyautata zaton barayin shannu a lardin Ankazobe suka tilasta musu shiga dakunan su ,daga bisani suka cinawa gidajen wuta.
Wallafawa ranar:
Masu kai dauki sun samu nasar ceto mutane uku daga cikin wutar, yayin da hukumomi suka kaddamar da bincike da nufin tattance barayin da suka aikata wannan barna a kauyen na Ankazobe.
Gwamnatin kasar ta tura da karin sojoji da yan sanda zuwa wannan yanki, al’amarin da gwamnati ta bayyana shi a matsayin bakin labari.
Wasu daga cikin yankunan kasar ta Madagascar sun kasance masu tattare da hatsari inda ake yawaitar hare-haren barayin shannu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu