Isa ga babban shafi

Tsohon shugaban Burkina Faso Campaore ya nemi afuwan iyalan Sankara

Tsohon shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore wanda kotun soji ta samu da laifin kashe tsohon shugaban kasar Thomas Sankara ta kuma yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai a bayan idan sa, ya nemi gafarar iyalan tsohon shugaban a karon farko.

Tsohon shugaban Burkina Faso, Blaise Compaoré.
Tsohon shugaban Burkina Faso, Blaise Compaoré. AFP - ISSOUF SANOGO
Talla

Wata wasika da ya rubuta wa gwamnatin kasar da kakakin ta Lionel Bilgo ya karanta wa jama’a ta ce, Compaore ya nemi gafarar jama’ar kasar Burkina Faso a kan duk wani kuskuren da yayi lokacin da yake shugabancin kasar, musamman iyalan ‘dan uwansa kuma abokinsa, Thomas Sankara.

Wasikar ta bayyana takaicin Compaore kan kura kuran da aka samu a karkashin mulkinsa, wanda ya ce ya dauki alhaki, saboda haka yana neman gafarar jama’a.

Compaore mai shekaru 71 ya hau karagar mulki a shekarar 1987 bayan juyin mulkin da ya hallaka shugaba Thomas Sankara, shugaban da ake ganin sa da kima a ciki da wajen Burkina Faso.

A watan Afrilun da ta gabata, kotun soji a Burkina ta yanke wa tsohon shugaban hukuncin daurin rai-da-rai saboda hannun da ya ke da shi wajen kashe Sankara.

Yanzu haka Compaore na gudun hijira a kasar Cote d’Ivoire tun bayan zanga zangar da ta raba shi da karagar mulki a shekarar 2014.

Shugaban mulkin sojin kasar mai ci Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba ya gayyaci Compaore ya koma gida domin sasanta jama’ar kasar da kuma shawo kan matsalolin 'yan ta’addan da suka addabe su.

Ziyarar da ya kai gida a watan Yuli ta haifar da cece kuce tsakanin 'yan siyasa da kungiyoyin fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.