Isa ga babban shafi

Blaise Compaore ya isa Burkina Faso bayan shekaru 8 a Cote d'Ivoire

Tsohon shugaban kasar Burkina faso Blaise Compoare ya isa birnin Ouagadougou a yau Alhamis bayan shafe shekaru 8 ya na gudun hijira a Cote d’Ivoire.

Tsohon shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore.
Tsohon shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore. AFP - THIERRY CHARLIER
Talla

Majiyoyin filin jirgin saman birnin sun tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Faransa isar tsohon shugaban wanda gwamnatin Cote d’Ivoire ta baiwa jirgin Sojin fadar shugaban kasa don mayar da shi gida.

Compaore mai shekaru 71 wanda ya gudu Cote d’Ivoire tare da samun mafaka zai halarci taron tsaffin shugabannin kasar ne da sabon shugaba laftanal kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba ya kira, shugaban da ya sha rantsuwar kama aiki bayan juyin muli cikin shekarar nan.

An gad ai yadda dandazon magoya bayan shugaban suka yi tururuwa zuwa filin jirgin saman birnin na Ouagadougou don tarbarsa.

Wannan ne karon farko da tsohon shugaban ke sanya kafa a kasarsa tun watan Oktoban 2014 lokacin da ya tsere makwabciyar kasar don samun mafaka bayan da rikici ya barke a kasar biyo bayan kudirinsa na shirin ci gaba da zama kan madafun iko bayan mulkin shekaru 27.

A shekarar 1987 ne Compoare ya kwace iko da ragamar mulkin kasar rana daya da kisan da aka yiwa Thomas Sankara, shugaban mulkin Sojin kasar.

Rahotanni sun ce Blaise Compoare ba zai dauki tsawon lokaci a Burkina Faso ba, zai shafe ‘yan kwanaki ne don halarta taron wanda Damiba ya gayyace shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.