Isa ga babban shafi

Amnesty ta bukaci bincike game da kisan gillar da fararen hula a yankin Oromia

Kungiyar Amnesty International ta bukaci a yi bincike game da kisan gillar da aka yi wa sama da fararen hula 400 a yankin Oromia na kasar Habasha cikin watan da ya gabata, inda tace masu shaidun gani da ido sun dora alhakin aika aikar a kan wata kungiyar ‘yan tawaye.

Masu zanga-zanga a yankin Oromo na kasar Habasha
Masu zanga-zanga a yankin Oromo na kasar Habasha Reuters/Tiksa Negeri
Talla

Tuni Kungiyar ‘yan tawayen Oromo ta musanta zargin, inda tace mayakan dake samun goyon baya daga gwamnati ne ke da alhakin kashe kashen da ya faru a ranar 18 ga watan yunin da ya gabata a yankin yammacin Habasha, abinda yayi sanadiyar tsananta hare hare a ‘yan watannin da suka gabata.

Shaidun gani da ido sun shaidawa kungiyar Amnesty international cewar Kazamin lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na safiya bayan wasu ‘yan bindiga da ake zargin mambobin kungiyar OLA ne suka far ma kauyukan Tole Kebele, kuma duk da shelar neman dauki da mazauna kauyukan suka yi, sai bayan awa 4 da faruwar lamarin jami’an gwamnati suka isa wurin.

Sanarwar da darektan Kungiyar a yankunan kudanci  da gabashin Afrika Deprose Muchena ya fitar na cewa, an kuma zargi mayakan Oromo da take hakkin bil adama fiye da zatto.

Muchena ya kuma ce dole a gudanar da kwakwarar bincike game da kisan gillar da yayi sanadiyar mutuwar mata da kananan yara.

Sanarwar na zuwa ne wata guda bayan kiran da shugaban hukumar kare hakkin bila dama ta majalisar dinkin duniya Michelle Bachelet tayi wa hukumomin Habasha su gudanar da bincike a kan kashe kashen kauyukan Tole.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.