Isa ga babban shafi

An kama mutane sama da 20 da ke shirin kutsawa Spain da karfin tuwo a Morocco

A jiya Asabar ‘yan sandan Morocco suka ce sun kama wasu mutane 25 da ake zargin da shirin tsallakawa zuwa cikin kasar Spain ba bisa ka’ida ba, bayan da yunkurin yin haka da wasu bakin haure suka yi a watan da ya gabata ya haifar da mummunan sakamako.

Bakin hauren da suka yi kokarin shiga Spain daga Morocco da karfin tsiyaa watan da ya gabata.
Bakin hauren da suka yi kokarin shiga Spain daga Morocco da karfin tsiyaa watan da ya gabata. AP - Javier Bernardo
Talla

A wata sanarwa, rundunar ‘yan sandan Moroccon ta ce ta kwace wasu karafa da aka kera musamman don hawa shinge daga wani babban shago a kasar, sai dai ba ta yi bayanin ko wane bangare na kasar Spain ne bakin hauren ke shirin afkawa.

Yankunan Ceuta da Melilla na kasar Spain na da iyaka ta kasa da kasar Morocco da ke nahiyar Afrika.

A watan da ya gabata bakin haure 23 ne suka mutu a yayin da suka yi yunkurin tsallakawa zuwa cikin kasar Spain da karfin tuwo.

Hukumomin Morocco sun ce suna daga cikin bakin haure sama da dubu 2 da suka yi kokarin tsallakawa shinge don su tsinci kansu a kasar Spain da ke nahiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.