Isa ga babban shafi

Cuta mai kama da Ebola ta bulla a Ghana

Ma’aikatar lafiya a Ghana ta sanar da bullar kwayar cutar da ake zargi ta  Marburg  ce mai alaka da Ebola, a yankin Ashanti na kudancin kasar a yau Juma’a, inda gwaji ya tabbatar mutane 2 sun harbu da ita.

 Nana Akufo-Addo, shugaban kasar Ghana.
Nana Akufo-Addo, shugaban kasar Ghana. © RFI/France24
Talla

Ma’aikatar lafiya ta Ghana ta ce gwaje gwajen da aka yi na samfurin jini da aka dauko daga mutane biyun da suka kamu da cutar a wata cibiyar bincike ta kasar Senegal sun nuna cewa mutanen na fama da cutar da ake zargi ta Marburg ce.

An zakulo wasu mutane 34 da da aka yi amannar sun yi  cudanya da wadanda gwaji ya tabbatar sun harbu da cutar, kuma an killace su, cewar wata sanarwa daga ma’aikatar.

Masana dai sun ce wannan kwayar cuta ba ta kai Ebola hadari ba, kuma ya zuwa yanzu babu allurar rigakafi ko kuma maganin cutar, wadda alamominta suka hada da zazzabi mai zafi da zubar jini a ciki da wajen wanda ya harbu da ita.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce idan aka tabbatar da lallai wadannan mutane sun harbu da kwayar cutar da ake zargi ta Marburg ce, zai kasance karo na farko kenan da aka samu bullar ta a Ghana.

Hukumar ta ce an samu mutum guda da ya kamu da wannan cuta a Guinea  a shekarar 2021.

A baya can, an samu bullar wannan cuta nan da can a kasashen Angola, Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, Kenya, Afrika ta Kudu da Uganda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.