Isa ga babban shafi

An cirewa Mali takukunman kasuwanci da tattalin arziki

Da  bude taron Kungiyar Kasashen Yankin Yammacin Afirka wato Ecowas karo na 61 a birnin Accra na kasar Ghana, taron ya mayar da hankali a game da halin da ake ciki a Mali, Burkina Faso da kuma Guinea, kasashe uku da kungiyar ta dakatar saboda juyin mulkin soji.

Taron Shugabanin Ecowas a Accra, na kasar Ghana
Taron Shugabanin Ecowas a Accra, na kasar Ghana © AP - Misper Apawu
Talla

Jim kadan bayan bude wannan taro, shugabannin kasashe mambobi a kungiyar suka shiga ganawa a asirce, inda suka cimma matsaya  na soke takukunman tattalin arziki da kasuwanci a kan kasar Mali, dangane da kasar Burkina Faso a maimakon shekaru uku majalisar soji ta sanar da tsaida shekaru biyu na rikon kwariya  tareda sallamar tsohon Shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore.

Shugabanin sun bayyana cewa ilahirin jakadodin kasashe aminan Mali za su koma aiki a bitrnin Bamako.

A jawabinsa wajen bude wannan taro dai, shugaban Hukumar Kungiyar ta Ecowas Jean-Claude Kassi-Brou, ya ce ‘’Yammacin Afirka yanki ne da ya rungumi tsarin dimokuradiyya, to amma halin da ake ciki a Mali, Burkina Faso da kuma Guinea na tabbatar da cewa dimokuradiyyar na fuskantar barazana a yankin’’.

Duk da cewa ba daya daga cikin shugabannin kasashen uku da aka gayyata domin halartar wannan taro, to sai dai manzannin musamman da kungiyar ta tura zuwa kasashen yanzu haka suna a birnin Accra don gabatar da rahotanninsu.

Ana dai kallon wannan taro a matsayin zakaran gwajin dafi, domin kuwa yayin da mahukunta a Mali ke fatan ganin kungiyar ta sassauta takunkuman da aka sanya wa kasar tun ranar 9 ga watan janairun da ya gabata, Taron na Accra na nuna ta yada kasashen Ecowas ke fatan ganin an kawo karshen zaman doya da man ja tsakanin su da gwamnatocin soji na wadanan kasashe uku.

An nada Shugaban kasar Guinea Bissau a mukamin Shugaban kungiyar kasashen ECOWAS a taron na Accra.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.