Isa ga babban shafi

Gabon da Togo sun shiga kungiyar kasashen renon Ingila ta Commonwealth

Kungiyar kasashe renon Ingila ta Commonwealth ta amince da zaman kasashen Gabon da Togo a matsayin sabbin wakilai, duk da cewa ba sa cikin jerin kasashen da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka.

Shugaban Rwandapaul kagame a yayin da yake jawabi a taron kungiyar CommonWealth.
Shugaban Rwandapaul kagame a yayin da yake jawabi a taron kungiyar CommonWealth. AFP - SIMON MAINA
Talla

Taron kungiyar dake gudana a Kigali na kasar Rwanda ya amince da bukatar kasashen biyu na zama mambobi, a cikin kungiyar da Sarauniya Elizabeth ta Biyu ke jagoranci, mai dauke da mambobi 54.

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya shaida wa manema labarai cewa taron shugabannin ya amince da takardun kasashen guda biyu, kuma yanzu haka sun zama wakilai kamar sauran mambobi 54.

Kasashen Gabon da Togo na daga cikin kasashe renon Faransa da suka zama wakilai a cikin Commonwealth tun bayan Rwanda a shekarar 2009.

Ministan harkokin wajen Togo, Robert Dussey ya ce shiga kungiyar ya bude wa kasar sa damar harkokin kasuwanci ga mutane sama da biliyan 2 da rabi da kuma wata damar samun ilimi musamman harshen Ingilishin da matasan kasar ke bukata.

Ministan ya shaida wa manema labarai cewar, zama wakiliya a kungiyar zai bai wa kasar damar fadada harkokin diflomasiyar ta da siyasa da kuma tattalin arziki, tare da kulla yarjejeniya da Birtaniya wadda ta fice daga kungiyar kasashen Turai.

Shugaba Ali Bongo  na Gabon ya bayyana cewar kasarsa ta kafa sabon tarihi wajen shiga kungiyar shekaru 62 bayan samun yancin kai, yayin da yake cewa matakin zai baiwa kasar sa damar bunkasa tattalin arzikin ta da diflomasiya da kuma al’adu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.