Belgium ta mayar da hakorin Lumumba ga iyalansa
Kasar Belgium ta mika hakorin tsohon shugaban Jamhuriyar Demokradiyar Congo Patrice Lumumba, wanda 'yan aware da sojojin haya na Belgium suka kashe, mutumin da ya yi shura wajen yaki da mulkin mallaka.
Wallafawa ranar:
Kisan Lumumba da kuma mummunan tarihin da Belgium ta yi a Demokradiyar Comngo ya kasance mai daure kai a tsakanin kasashen biyu.
An sanya hakorin a cikin wani akwati da aka lullube da wani kyalle mai launin tutar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, domin karrama Lumumba.
Lumumba mai sukar salon mulkin Belgium, ya zama firaministan kasarsa na farko bayan samun 'yancin kai a shekarar 1960.
Kisan Lumumba
An kashe shi a ranar 17 ga Janairun 1961, yana da shekaru 35, a yankin kudancin Katanga, bisa goyon bayan sojojin haya na Belgium, inda aka narkar da gawarsa da sinadari mai guba.
Amma daya daga cikin wadanda suka kashe shin, dan kasar Belgium ya ajiye hakorin a matsayin tarihi.
Har yanzu dai ana ci gaba da gudanar da bincike kan laifukan yaki amma biyu daga cikin jami'an da suka kashe shi suna raye.
Kisan mutane da dama
Masana tarihi sun ce miliyoyin mutane ne aka kashe, ko aka batar da su ko kuma suka mutu sakamakon kamuwa da cutar, yayin da aka tilasta musu tara roba a karkashin mulkin Belgium. Haka kuma an mamaye kasar ne saboda arzikin ma'adinai, katako da hauren giwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu