Isa ga babban shafi

Sarki Philippe na Belgium ya yi nadamar abin da kasarsa ta yi a Congo

Sarki Philippe na Kasar Belgium ya bayyana nadama dangane da illar da mulkin mallakar da kasarsa ta haifar a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo wanda ya kai ga rasa dimbin rayuka a ziyarar kwanaki 6 da yake yi yanzu haka.

Shugaban Congo Félix Tshisekedi tare da Sarki Phillipe na Belgium da ke ziyara a Congo
Shugaban Congo Félix Tshisekedi tare da Sarki Phillipe na Belgium da ke ziyara a Congo AFP - ARSENE MPIANA
Talla

Yayin da yake jawabi a kofar majalisar dokokin Kinshasa, Sarkin ya bayyana alhininsa kamar yadda ya yi shekaru 2 da suka gabata akan matsalar nuna banbanci da wariyar jinsi da kuma azabtarwar da mulkin mallakar ta haifar a Congo wadda tayi sanadiyar mutuwar miliyoyin jama’a.

Sarki Philippe ya bayyana banbancin dangantar da aka samu tsakanin Belgium da Congo a matsayin wadda ta haifar da cin zarafi da kuma kunyata jama’ar kasar.

Philippe ya bayyana al’ummar kasar Belgium da dama a matsayin masu kaunar Congo da jama’ar ta soyayya ta gaskiya.

Sarki Leopold II wanda ‘dan uwa ne ga Kakan Sarki Philippe ya jagoranci kasar Congo kamar kadarar sa tsakanin shekarar 1885 zuwa 1908 kafin daga bisani ta zama wani yanki da Belgium ta yiwa mulkin mallaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.