Isa ga babban shafi

Sakataren MDD zai ziyarci wasu kasashen yammacin Afirka

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, zai ziyarci wasu kasashen yammacin Afirka daga karshen wannan mako domin bayyana irin illar da yakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine ya yiwa nahiyar Afirka da wasu muhimman batutuwa.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. REUTERS - VALENTYN OGIRENKO
Talla

Bayan ziyarar da ya kai zuwa Rasha da Ukraine a cikin makon da ya kare, Guterres zai isa Senegal da yammacin ranar Asabar don ziyarar aiki a ranakun 1 da 2 ga Mayu.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar zai kuma yi tattaki zuwa Nijar inda zai kasance har zuwa ranar 3 ga watan na Mayu, kafin ya kammala rangadinsa a Najeriya a ranakun 3 da 4 ga dai watan.

Bayan tattaunawa da shugabannin kasashen uku da zai ziyarta, Guteress zai kuma gana da wakilan kungiyoyin fararen hula da shugabannin addinai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.