Isa ga babban shafi
Kenya-Tattalin arziki

Kenya ta gabatar da kasafin kudi mafi yawa na dala biliyan 28

Gwamnatin Kenya ta gabatar da kasafin kudin kasar da ya tasamma Dala biliyan ashirin da takwas, da nufin farfado da tattalijn arzikin kasar da ya shiga cikin wani yanayi sakamakon annobar Corona.

Shugaba Uhurru Kenyatta na Kenya.
Shugaba Uhurru Kenyatta na Kenya. AP - Gonzalo Fuentes
Talla

Kasafin na shekarar 2022-2023 da aka gabatar watanni hudu gabanin babban zaben kasar da ke tafe, an warewa bangaren zuba jari da ayyukan raya kasa biliyoyin daloli, wanda mafi yawa daga ciki, kasar China ta tallafawa gwamnatin Uhuru Kenyatta.

Sama da mutum dubu dari bakwai ne suka rasa ayyukansu a shekarar 2020 a Kenya, yayin da suke cikin wani hali saboda hauhawar farashin kayayyaki, musamman abinci da tsadar mai, ga kuma fari da ya shafi yankuna da dama na kasar.

Idan har majalisar dokokin kasar ta amince da kasafin, bangaren lafiya, gidaje, abinci da kuma masana’antu za a yi amfani da su wajen cike gibin da annobar Corona ta haifar.

Kasar dai ta samu tasgaro a bangaren samun kudin shiga ta bangaren yawon bude idanu da nan ne tafi samu, saboda annobar Covid-19.

Wannan shi ne kasafin kudi na karshe da aka gabatar a karkashin shugabancin Uhuru Kenyatta, yayin da kundin tsarin mulkin kasar ya kayyade adadin wa'adin shugaban kasa zuwa biyu akan kujerar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.