Isa ga babban shafi
Kenya

Kenya na binciken kan kwaroron roba da magunguna da aka sace mata

Mahukunta a kasar Kenya sun kaddamar da bincike bayan da aka gano wasu dubban kayyakin kiwon lafiya da aka bai wa kasar a matsayin tallafi amma ana sayar da su cikin kasuwanni.

Shugaban kenya Uhuru Kenyatta.
Shugaban kenya Uhuru Kenyatta. REUTERS - MONICAH MWANGI
Talla

Wadannan dai kayayyaki ne da suka hada da kwararon roba domin kariya, gidajen sauro da kuma magunguna, wadanda  asusun Global Fund da ke Geneva ya bai wa kasar don yaki da cuta mai karya garkuwar jiki, da tarin fuka da kuma zazzabin malariya a kasar.

A jimilce dai Asusun ya ware dala bilyan daya da milyan 400 ne don samar da wadannan kayayyaki da kuma raba su a cikin kasar ta Kenya.

To amma wani bincike da aka gudanar a baya-bayan nan, ya tabbatar da cewa kwararon roba miliyan daya da dubu dari, da gidajen sauro sama da dubu 900, da dimbin magungunan yaki da cutar HIV da na tarin TB ne aka sace sannan aka rika sayar da su a cikin kasuwannin kasar.

An bayyana cewa kayayyakin da aka sace a hukumar da ake kira KEMSA kimarsu za ta kai dala dubu 91, to sai dai wasu bayanan na cewa adadin ya zarta haka.

Ko a shekara ta 2020, an bankado wani sama-da-fadi na dala milyan 400 da aka yi karkashin wani asusun musamman da aka kafa don yaki da cutar covid-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.