Isa ga babban shafi
Kenya

Kotun kolin Kenya ta soke dokar haramta saidawa da cin naman Jakai

Babbar kotun Kenya ta soke hukuncin haramta yankawa tare da sayar da naman Jakai a kasar domin ci ko kuma sarrafa shi.

Wata 'yar kasar Kenya yayin safara da Jakanta a yankin Kajiado dake kudancin kasar.
Wata 'yar kasar Kenya yayin safara da Jakanta a yankin Kajiado dake kudancin kasar. AP - Ben Curtis
Talla

A shekarar 2020 ne dai gwamnatin kasar ta Kenya ta haramta cin naman Jakan ko sayar da su, matakin da wasu ‘yan kasar suka ruga babbar kotu domin neman soke shi, saboda hasarar makudan kudaden shigar da suka ce dokar ya janyo musu.

Kafin gwamnatin Kenya ta haramta saidawa da cin naman Jakuna, akwai manyan gidajen yanka na abbatuwa hudu a sassan kasar da a cikinsu ake yanka Jakan akalla dubu 1 kowace rana.

Sai dai alkaluman baya bayan nan da gwamnatin kasar ta wallafa sun nuna cewar adadin Jakan dake Kenya sun ragu daga miliyan 1 da dubu 800 shekaru 10 da suka gabata zuwa, miliyan 1 da dubu 200 a halin yanzu, daya daga cikin hujjojin da take amfani dasu wajen kare matakin ta na haramta yankawa da saida naman dabbobin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.