Isa ga babban shafi
Mali -ECOWAS/CEDEAO

Kotu ta yi umurnin dakatar da takunkuman da aka laftawa Mali

Wata kotu a Afirka ta Yamma ta ba da umarnin dakatar da takunkumin da aka kakaba wa Mali, sakamakon jinkirin da aka yi na zabukan kasar, a wani mataki na diflomasiyya da ba kasafai aka saba gani ba, ga gwamnatin mulkin sojan kasar.

АShugaban gwamnatin sojin Mali, Assimi Goita.
АShugaban gwamnatin sojin Mali, Assimi Goita. AFP - NIPAH DENNIS
Talla

Kotun Kungiyar Tattalin Arziki ta Afirka ta Yamma UEMOA ta bayar da wannan umarni ne a jajibirin taron koli kan kasar Mali da ke fuskantar matsin lamba na maido da mulkin demokradiyya bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 2020.

Bayan da gwamnatin mulkin soji ta ba da shawarar ci gaba da mulki har na tsawon shekaru biyar, ECOWAS ta kakaba wa kasar da ke yankin Sahel takunkumin tattalin arziki da diflomasiyya a watan Janairu.

Babu tabbas ko hukuncin dakatarwar da kotun UEMOA ta yanke zai kai ga dage takunkumin da aka kakabawa kasar nan take.

Hukumomin mulkin sojan Mali na kallon takunkumin a matsayin wanda ya saba wa doka inda a watan Janairun da ya gabata suka sha alwashin kalubalantarsu a kotunan duniya.

A cewar hukuncin kotun, lauyoyin gwamnatin Mali sun shigar da kara ne domin a haramta takunkumin da aka kakabawa kasar.

Kotun ta yanke hukuncin dakatarwa ne, inda ta yi nuni da hujjojin masu tushe na shari’a da kuma illar tattalin arzikin da takunkumin zai haifar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.