Isa ga babban shafi

Adadin mutanen da guguwar Batsirai ta kashe sun kai 120

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon mahaukaciyar guguwar da ta afkawa kasar Madagascar da aka yiwa suna Batsirai ya kai 120, kuma akasarin wadanda suka mutu sun fito ne daga yanki guda.

Des habitants sur une route endommagée suite à un glissement de terrain lors du passage du cyclone Batsirai qui a touché le sud-est de Madagascar, le 6 février 2022.
Des habitants sur une route endommagée suite à un glissement de terrain lors du passage du cyclone Batsirai qui a touché le sud-est de Madagascar, le 6 février 2022. REUTERS - ALKIS KONSTANTINIDIS
Talla

Hukumar agajin gaggawa ta kasar tace sama da kashi 70 na mamatan sun fito ne daga yankin Ikongo dake kusa da gabashin tsibirin dake kogin India.

Una brigada de limpieza retira ramas de una carretera en el distrito de Tanambao tras el paso del ciclón Batsirai, el 8 de febrero de 2022 en Mananjary, en la costa este de Madagascar
Una brigada de limpieza retira ramas de una carretera en el distrito de Tanambao tras el paso del ciclón Batsirai, el 8 de febrero de 2022 en Mananjary, en la costa este de Madagascar Rijasolo AFP/Archivos

Gwamnatin kasar tace guguwar ta shafi mutane 125,000 wajen raba su da matsugunan su, yayin da jami’an jinkai ke can suna taimaka musu wajen samar musu da matsuguni da kuma abinda zasu ci.

La plus grande difficulté pour atteindre les zones sinistrées, dont le district très touché d'Ikongo, est l'état des routes, comme ici la RN25 à Ranomafana, le 7 février 2022.
La plus grande difficulté pour atteindre les zones sinistrées, dont le district très touché d'Ikongo, est l'état des routes, comme ici la RN25 à Ranomafana, le 7 février 2022. AFP - RIJASOLO

Kasar Madagascar na daya daga cikin masu fama da matsalar talauci a duniya, yayin da sama da kashi 42 na yara kasar ke fama da matsalar yunwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.