Kwamitin tsaron MDD zai tattauna kan rikicin kasar Sudan
Wasu majiyoyin jami’an diflomasiyya sun ce a ranar larabar da ke tafe, kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai tattauna kan halin da ake ciki a Sudan, inda dubban ‘yan kasar ke cigaba da zanga-zangar adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi.
Wallafawa ranar:
Majiyoyin sun bayyana cewar kasashe 6 daga 15 masu kujerar dindindin a kwamitin tsaron ne suka nemi yin taron akan abubuwan da ke wakana a Sudan, kuma ganawar ta su za ta gudana ne a sirrance.
Wani jami'i da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, ba a sa ran kwamitin tsaron ya fitar da matsaya guda kan tashin hankalin kasar ta Sudan, la’akari da cewar kasashen China da Rasha za su hau kujerar naki.
A baya dai Rashan da China sun sha jaddada cewa halin da ake ciki a Sudan na rudani tun bayan da sojoji suka kwace iko a ranar 25 ga watan Oktoba, lamari ne na cikin gida, kuma ba ya barazana ga tsaron kasa da kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu