Jami'an tsaro sun kashe masu zanga-zanga 4 a Sudan
Majiyoyin kiwon lafiya a Sudan, sun tabbatar da mutuwar mutane 4 bayan da jami’an tsaro suka yi amfani da karfi don tarwatsa tarzomar da aka gudanar yau alhamis a biranen Ondurman da kuma Khartoum fadar gwamnati.
Wallafawa ranar:
Dubun dubatar mutane ne suka fito domin kalubalantar gargadin da mahukunta suka yi kan cewa ka da wanda ya fito da nufin gudanar da tarzomar adawa da gwamnatin hadaka da ta hada sojoji da fararen hula a kasar.
Majiyoyin kiwon lafiya a asibitin Arbain das ke Ondurman, sun tabbatar da cewa an shigar da gawarwakin mutane da dama a asibitin, yayin da a hannu daya jami’an tsaro suka gargadi asibiti da ka da ta kuskura ta bai wa motocin daukar marasa lafiya damar shiga sauke wadanda suka samu raunuka.
Tun da farko dai an baza dimbin jami’an tsaro kan titunan Khartum da kuma Ondurman don tabbatar da cewa ba a gudanar da wannan zanga-zanga ba, amma duk da haka sai da dubban mutane suka fito kan tituna.
Su dai masu wannan tarzoma na jaddada adawarsu ne kan cewa, Sudan ba ta bukatar gwamnatin hadaka da za ta kunshi sojoji da fararen hula, zanga-zangar da aka share tsawon watanni ana yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu