Isa ga babban shafi
Kamaru

Kotun Kamaru ta saki daliban da aka daure saboda barkwanci kan Boko Haram

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta ce an saki wasu dalibai uku 'yan kasar Kamaru da aka yankewa hukuncin daurin shekaru goma-goma a gidan Yari bisa samunsu da yin barkwanci a kan kungiyar Boko Haram.

Hoton gudumar Kotu ko kuma ta Alkali manta sabo.
Hoton gudumar Kotu ko kuma ta Alkali manta sabo. © REUTERS/Andrew Kelly/Illustration
Talla

Wata kotun sojin kasar Kamaru ce dai ta samu Fomusoh Ivo Feh, da Afuh Nivelle Nfor, da kuma Azah Levis Gob da laifin rashin la'antar bayanan da ke da alaka da ta'addanci a watan Nuwamban shekarar 2016 bayan da suka yada wani sakon raha game da 'yan Boko Haram a wayoyinsu.

Amnesty ta ce an sako daliban, wadanda ke tsare tun watan Janairun 2015 a karshen mako bayan da kotun kolin kasar ta Kamaru ta rage hukuncin daurin zuwa na shekaru biyar.

A cikin wata sanarwa da Amnesty ta fitar ta ce, daliban uku sun yi amfani ne da 'yancin fadin albarkacin baki kawai, dan haka bai kamata a kama su ba tun da farko.

Kungiyar ta kara da cewa sakon da daliban suka yi musayarsa, yayi tsokaci ne kan wahalar samun aiki mai kyau ba tare da samun kwarewa sosai ba.

A karshen shekarar 2014, daya daga cikin daliban ya samu sakon kar ta kwana daga wani abokinsa yana mai cewa Boko Haram na daukar matasa aiki idan sun ci jarabawar darussa akalla hudu, sakon da daga bisani wani malaminsu ya gani, ya kuma nunawa ‘yan sanda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.