Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Habasha ta yi ikirarin kwato wani gari daga hannun 'yan tawaye

Kasar Habasha ta sanar da cewa dakarunta sun sake kwatar wani gari a kusa da babban birnin kasar daga hannun ‘yan tawayen Tigray da sukayi ikirarin kwace shi a makon da ya gabata, a wani bangare na yankurin kama Addis Ababa.

Hoton zane kan ikirarin Franminsta Abiy Ahmed na Habasha dake cewa ya jagoranci sojoji zuwa fagen daga domin fafatawa da 'yan tawaye (25/11/2021)
Hoton zane kan ikirarin Franminsta Abiy Ahmed na Habasha dake cewa ya jagoranci sojoji zuwa fagen daga domin fafatawa da 'yan tawaye (25/11/2021) © FMM-RFI
Talla

Kakakin gwamnatin kasar, Legesse Tulu wanda ya sanar da matakin, ya ce Shewa Robit na daga cikin kananan garuruwan da dakarun da ke biyayya ga Firanminista Abiy Ahmed suka kwato, wanda a makon da ya gabata ya sanar da cewa zai jagoranci sojojin nasa zuwa fagen daga, yayin da bayanai ke cewa yaki ya sake barkewa a akalla bangarori uku a kasar.

Da yake tabbatar da matakin yayin sanarwa a gidan talabijin din kasar kakakin gwamnatin yace a gumurzun da akayi a dagar  Shewa, dakarun gwamnati sun yi nasarar  sake maido da ikon garuruwan Mezezo da Molale da Shewa Robit da kuma Rasa da kewaye daga hannun ‘Yan tawayen TPLF na yankin Tigray dake dauki ba dadi da gwamnatin Abiy tun cikin watan Nuwambar 2020.

Rikicin ya dauki sabon salo tare da tada hankalin kasar da ma duniya baki daya tun cikin watan da ya gabata, lokacin da kungiyar ta TPLF ta yi ikirarin kwace manyan garuruwan irinsu Dessie da Kombolcha, da ke kan titin zuwa babban birnin kasar.

Kokarin ‘yan tawaye na kwace Addis Ababa babban birnin kasar ya sanya kasashen Amurka da Faransa da Birtaniya da wasu kasashe kira ga 'yan kasarsu da su gaggauta ficewa daga Habasha, duk da cewa gwamnatin Abiy ta ce nasarar ‘yan tawaye bata taka kara ta karya ba, tare da tabbatar da cewa birnin nada cikekken tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.