Facebook da Twitter sun yi kashedi ga hukumomin Habasha
Fira Ministan Habasha ya bukaci ‘yan kasar sa da su kasance cikin shirin sadaukar da rayukansu da ceton kasar daga barazanar tsaron da take fuskanta. Yanzu kam kafoffin sada zumunta na Facebook da Twitter sun sanar da dauka matakan sa ido kan wasu daga cikin kalaman Firaministan kasar da kan iya tunzura jama’a.
Wallafawa ranar:
Shafin sada zumunta na Facebook ya sanar da goge wasu daga cikin sakonnin Firaminista Aby Ahmed,lamarin da ya fusata hukumomin wannan kasa.
A baya bayan nan ne dai Amurka ta baiwa jami’an diflomasiyyar ta umarnin ficewa daga Habasha, yayin da yakin da ake gwabzawa tsakanin ‘yan tawayen Tigray da dakarun gwamnati ke kara tsananta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu