Isa ga babban shafi

Amurka da wasu kasashe sun umurci yan kasar su da su fice daga Habasha

Amurka, Sweden da Noway su umurci yan kasar  su dake zaune a Habasha da su fice daga kasar ba tareda bata lokaci ba ,kiran na Amurka dake zuwa a wani lokaci da yan tawayen  Tigray na TPLF ke ci gaba da sa kai zuwa babban birnin kasar Habasha da shirin kiffar da gwamnatin Firaminista Aby Ahmed.

Mayakan TPLF a Tigray
Mayakan TPLF a Tigray Yasuyoshi Chiba AFP/File
Talla

Majalisar Dimkin Duniya ta kira kungiyoyi dake dauke da makamai da dakarun gwamnatin kasar da su cimma matsaya ta gari, tareda cimma tsagaita wuta cikin gaggawa.

Yan tawayen Tigray
Yan tawayen Tigray AFP - YASUYOSHI CHIBA
Kungiyar Tawayen Tigray People's Liberation Front (TPLF) da ta shafe shekara guda tana yakar gwamnatin Firaiminista Abiy Ahmed, ta yi ikirarin samun gagarumar nasara a mamaye wasu yankuna a 'yan kwanakin nan, tare da kawayenta na 'yan tawayen Oromo Liberation Army (OLA).
Wasu sojojin kasar Habasha yayin atasaye a yankin Amhara, ranar 14 ga Satumban shekarar 2021.
Wasu sojojin kasar Habasha yayin atasaye a yankin Amhara, ranar 14 ga Satumban shekarar 2021. © Amanuel Sileshi AFP/File
Yan tawayen TPLF da kawancen su na kan hanyar su ta kama babban birnin kasar Habasha,sun kama kemisse dake da nisan kilometa 325 da babban birnin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.