Isa ga babban shafi
Sudan

Jami'an tsaron Sudan sun kashe mutane 2 yayin zanga-zangar kin jinin gwamnati

Likitoci a Sudan sun ce jami'an tsaro sun kashe mutane biyu yayin zanga-zangar adawa da juyin mulkin da sojoji suka sake yi a makon da ya gabata.

Masu zanga zangar adawa da juyin mulkin sojoji a Sudan.
Masu zanga zangar adawa da juyin mulkin sojoji a Sudan. © REUTERS - MOHAMED NURELDIN ABDALLAH
Talla

Kwamitin likitocin Sudan mai zaman kansa ya ce an kashe masu zanga-zangar ne a birnin Omdurman, duk kuwa da gargadin manyan kasashen duniya da suka bukaci sojoji su mutunta hakkin dan Adam.

Kisan baya-bayan nan a birnin na Omdurman ya kai adadin wadanda suka mutu tun bayan barkewar zanga-zangar kin jinin gwamnatin sojojin a ranar Litinin zuwa  mutane 11, yayin da wasu kimanin 170 suka jikkata.

Masu zanga-zanga a Sudan.
Masu zanga-zanga a Sudan. - AFP

Dubban masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin sojoji a kasar Sudan ne suka fantsama kan tituna a ranar Asabar, domin nuna goyon bayansu ga tsarin mulkin dimokradiyya a kasar wanda sake juyin mulkin da sojoji suka yi ya dakile.

Zanga-zangar ta zo ne kusan mako guda bayan da sojoji suka tsare shugabannin farar hula na Sudan a ranar Litinin da ta gabata, tare da rusa gwamnatin rikon kwaryar dake jagoranci, da kuma ayyana dokar ta baci, lamarin da ya janyowa sojojin Allah wadai daga kasashen duniya.

Duk da zubar da jinin da ake samu ne kuma masu shirya zanga-zangar suka sha alwashin jagorantar sake fitar mutane akalla miliyan 1, don nuna adawa da kwace madafun iko da sojoji ke yi, kwatankwacin zanga-zangar da ta kai ga hambarar da gwamnatin tsohon shugaba Omar al-Bashir a shekarar 2019.

Dubban mutane ne suka taru a Khartoum, babban birnin Sudan da kuma garuruwan Omdurman da Khartoum ta Arewa, a cewar shaidu da wakilan kamfanin dillancin labarai na AFP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.